Bayani
Wannan shiri na [i]:her(e), an qirqiro shi ne domin tunkarar harkokin tsarin zayyanar gine-gine a matsayin dandali da kuma mataki na nuna bajinta. Waxannan bayanan, waxanda aka tsara su dalla-dalla, kuma mataki-mataki, sun zama wata hanya da ake bi wajen nuna xaukaka ga wasu koqasqantarwa; yayin da kuma ake yin amfani da shi wajen nuna qwarewa a cikin sana’ar.
Ta hanyar tsari na musamman na saay/yaas*, wasu ’yan asalin Afrika su huxu, sun kawo tasu manhajar a qarqashin tsarin Saison Africa 2020. A qarqashin wannan tsarin, wanda aka qirqiro shi a manhajar ba-ni-in-ba-ka, sun samar da dandali a yanar sadarwa ta zamani, domin havaka ilmi da kyautata aiki, ta hanyar tuntuvar juna akai-akai da qara sanin juna.
Mutanen da suka kawo wannan shirin mata ne masana, kuma qwararru ‘yan Afirka mazauna qasashen waje, waxanda a koyaushe akan ware su a cikin harkokin ilmi, amma kuma ayyukansu kan shafi fannoni da yanayi da halayya daban-daban.
Sindi, Anthony, Abengowe, Yehouessi/Yehouessi, Abengowe, Anthony, Sindi.
GAYYATA
“Mafarkin abubuwan da ba su wakiltar mu, sai dai abubuwan da turawa fararen fata suke hasashe game da mu. Tunanin irin abubuwan da turawan ne suka rasa, su ne ake jinginawa da mu, kamar waxannan su ne halayyarmu ta zahiri. Sai dai kuma wannan bai dame mu ba.” - Grada Kilomba.
Zuwa ga ‘yan’uwa da abokan aiki,
Yayin da aka dora wa mata nauyin bayyanashirin zayyanar gine-gine na “Saison Africa 2020 Architecture”, qungiyar saay/yaas ta sami qwarin gwiwa daga irin hikimomin ’yan Afirka da na ’yan qasashen waje mazauna turai, waxanda ke nuna qwazonsu da fasaharsu; tare kuma da wargaza irin mummunar fahimta da tunanin bai xaya da ake da su game da nahiyar Afirka, “...ta hanyar bayyana wa waxanda a da ba su sami damar ganin hakan ba”. Qungiyar saay/yaas ta gudanar da baje kolin fasahar zayyane-zayyanen ne domin ya zama manuniya; daga baya ne aka samar da dandalin her(e) a kafar sadarwa ta yanar gizo.
Wata kalmar bayani “ita ta ke bayyanar da wani bayanin kuma”, “ta hanyar nuni da dangantakar abin da wuri, lokaci, dalili, yanayi, zurfinsa, da sauran su”. Don haka amfani da kalmar “her(e) da aka yi a sunan dandalin, wanda akan karanta a matsayin “her”, watau “ita”, yana nuni da dangantaka mai sarqaqqiya ta fuskar wuri da lokaci, wadda ke akwai tsakanin kafa waje na aiki da kasancewar ta mace, ’yar Afirka mai zama a turai, a cikin abokan aikin da aka saba ganin yawancin su maza ne, fararen fata, masu hannu da shuni, kuma masu bin tsarin qasashen yamma wajen gudanar da sana’ar zayyanar gidaje.
Baya ga wannan, her(e) rayayyen dandali ne, wanda yake cike da fasaha, mai bayyana shawarwari, wanda kuma yake shirya tambayoyi akan fahimta da fannoni daban-daban na aikin zayyanar gini. Haka nan, a kowane lokaci dandalin yana samar da bayanai dangane da dangantaka da ke akwai tsakanin qwararru, da irin ayyukansu, da yanayin sana’arsu, da kuma fasahohin da suka shafi Afirka da ’yan asalin nahiyar mazauna qasashen waje. Dandalin ya samar da dama ga mata baqaqen fata, waxanda ke ta qaruwa, domin su sadu da juna cikin aminci, su kyautata hulxarsu, tare da haxa kai wajen nema wa kansu kyakkyawar makoma.
Don haka muna gayyatar ku domin ku bayyana kawunanku, ta hanyar kawo labarun ayyukanku, da bayyana tunaninku, da qwarewarku, tare da abubuwan da ku ke so ko jin tsoro, ko na raha (waxanda za a iya aikatawa a aikace, ko saurare, ko a rubuce). Waxannan sun haxa da ayyukan da aka kammala, ko ake shiryawa, ko tambayoyi, ko mahawarori; ba tare da gindaya wani shamaki ba. Za a iya kawo irin wannan gudummuwa a bayyane, ko kuma ba tare da ambaton sunan mai bayarwa ba. Haka kuma za ku iya bayyana a qarqashin wani kamfani ko ofishin da ku ke aiki, a matsayin qungiya ko kuma da sunanku. Muna roqon ku da ku yaxa wannan bayani ga sauran waxanda ba su sami wannan sanarwa ba daga Afrika da sauran wurare a qasashen waje, don su kawo nasu bayanan. Ta haka sannu a hankali sai a tattara dukkan masana da qwararru guri xaya daga fannoni daban-daban a cikin wannan sana’ar ta zayyanar gine-gine, domin a tafi tare.